AN KARA ZUBAR DA KIMA DA MUTUNCIN NIGERIA A IDON DUNIYA Kowa dai yana sane da abinda ya faru kwanaki kadan da suka wuce tsakanin mahukuntan Nigeria da kamfanin Binance wanda ake hada-hadar kudin Crypto a cikinsa A wani yunkuri na borin kunya daga mahukuntan Nigeria sunce wai Binance ne ya haddasa hauhawar farashin Dala, don haka suka dauki mataki kan Binance, suka dakatar da P2P garemu 'yan Nigeria da muke mu'amala da Binance Exchanger Daga bisani Mahukuntan Nigeria sun kama ma'aikatan Binance guda biyu, amma ance wai daya daga cikinsu ya tsere ba tare da anyi bayanin hanyar da yabi yatsere ba Kwatsam yau kuma sai Shugaban gudanarwan kamfanin Binance ya saki labari cewa wasu daga cikin mukarraban Gwamnatin Nigeria sun bukaci kamfanin Binance ya basu cin hanci na kudi Dalar Amurka Miliyan 150, kusan Naira Biliyan 200 kenan a kudin Nigeria wai zasu gyara matsalar dake tsakanin Binance da Gwamnatin Nigeria Amma Binance sunki yadda su bada cin hancin, sukace suna so a warware ...
Alihsan Company limited