Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta samar wa maniyyatan Nijeriya ragin kudaden aikin hajjin 2024 daga gwamnatin Saudiyya.
Rage kudaden, a cewar Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar, ya samu ne daga ɓangaren farashin kudin jirgi, da masauki da kuma zaman Masha’ir.
Usara ta bayyana cewa an samu wannan nasara ne a lokacin da Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya jagoranci tawagarsa zuwa shirye-shiryen aikin Hajjin 2024 tare da mai da hankali kan rage farashin hidimomin da za a yi wa maniyyata daga Najeriya a ƙasar Saudiyya.
Ta yi bayanin cewa shugaban ya gabatar da rokonsa na rage farashi kan yanayin tattalin arzikin duniya da ya shafi maniyyata, mahajjata daga Najeriya sakamakon kulle-kullen da ya faru lokacin COVID-19 da yakin da ake yi a Turai.
Usara ta yi bayanin cewa farashin masauki a Madina ya ragu daga SR 2,080 (Ryal Saudi) a 2023 zuwa Riyal 1,665 a bana. Hakazalika, farashin masauki a Makka ya dawo Riyal 3000 akan Riyal 3,500 na shekarar da ta gabata.
Ta kara da cewa maniyyatan aikin hajjin 2024 za su biya Riyal 4,770 na kunshin Masha’ir (VAT inclusive) akan Riyal 5,393 da mahajjatan bara suka biya.
Dangane da kudin jirgi, Hukumar ta sami damar doke farashin tare da rangwamen dala 138 daga abin da aka biya a bara.
Comments
Post a Comment