AN KARA ZUBAR DA KIMA DA MUTUNCIN NIGERIA A IDON DUNIYA
Kowa dai yana sane da abinda ya faru kwanaki kadan da suka wuce tsakanin mahukuntan Nigeria da kamfanin Binance wanda ake hada-hadar kudin Crypto a cikinsa
A wani yunkuri na borin kunya daga mahukuntan Nigeria sunce wai Binance ne ya haddasa hauhawar farashin Dala, don haka suka dauki mataki kan Binance, suka dakatar da P2P garemu 'yan Nigeria da muke mu'amala da Binance Exchanger
Daga bisani Mahukuntan Nigeria sun kama ma'aikatan Binance guda biyu, amma ance wai daya daga cikinsu ya tsere ba tare da anyi bayanin hanyar da yabi yatsere ba
Kwatsam yau kuma sai Shugaban gudanarwan kamfanin Binance ya saki labari cewa wasu daga cikin mukarraban Gwamnatin Nigeria sun bukaci kamfanin Binance ya basu cin hanci na kudi Dalar Amurka Miliyan 150, kusan Naira Biliyan 200 kenan a kudin Nigeria wai zasu gyara matsalar dake tsakanin Binance da Gwamnatin Nigeria
Amma Binance sunki yadda su bada cin hancin, sukace suna so a warware matsalar ta hanyar doka, yanzu wannan labarin shine yake trending a duniya
Kunga an kara zubar mana da kima da mutuncin Kasarmu Nigeria a idon duniya
Mun fahimci cewa dama an nemi daukar mataki kan Binance ne don wasu tsirarun mukarraban Gwamnati su samu kudi amma hakarsu bata cimma ruwa ba, tonon asiri ya biyo baya
To da wannan muke kira ga Maigirma Mai bawa shugaban Kasa shawara akan tsaro Malam Nuhu Ribado akan ya binciki wadanda suka nemi Binance su bada cin hanci, ayi gaggawan rabasu da Gwamnatin Tinubu, inda hali a dauki matakin da ya dace a kansu
Allah Ya sauwake
Comments
Post a Comment