Skip to main content

BABU INDA NACE NAFI ƳAN NIGERIA SHAN WAJALAR TSADAR RAYIWA

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa.

A jiya Laraba ne dai wani labari ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ake cewa wai Dangote ya ce ya fi yan Nijeriya jin raɗaɗin tsadar rayuwa.

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin sa ya fitar a jiyan, Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su .

Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya.

“Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafe mu”, inji Sanarwar.

Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.”

Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da takin zamani da kuma tatar man fetur. A bangaren kayan abinci kuma, Kamfanin na sarrafa sikari, gishiri da kayan dandanon girki ne kadai.

“Muma muna siyan muhimman kayan abinchi a kasuwa kamar yarda kowa ke siya don amfanin kanmu da kuma bayarwa wajen ciyar da al’umma.” Dangote.

Shugaban kamfanin yayi mamakin yadda ake neman haddasa sabani tsakanin Kamfanonin Dangote da bangaren gwamnatin tarayya, inda yace shi dan kasuwa ne ba dan siyasa ba, don haka babu inda yayi maganar kalubalantar Gwamnatin tarayya.

“Kamfaninmu ya kasance me bin dokokin kasa a koda yaushe tare da neman sauki ga al’umma da fatan alheri.”

Saboda haka, sanarwar ta nemi Yan Nigeria su guji daudar sakon da yake ba daga kamfani yake kai tsaye ba, tare da yada rade-radi da jita-jita

DailyNigeria.com ce ta yawaita.


LEAVE A REPLY

Latest article


Comments

Popular posts from this blog

SHAWARA MAI MUHIMMANCI GA WAƊANDA SUKE AIKI DA TELEGRAM

SHAWARA MAI MUHIMMANCI GA WADANDA SUKE AMFANI DA TELEGRAM ACCOUNT  Datti Assalafiy  ✍️ Yanzu dai a duniya shafin sada zumunta na Telegram shine yake tashe, sakamakon cewa yanzu babu wani shafin sada zumunta da ya bude hanyar da talaka fakiri zai samu alheri kamar Telegram Ko baka da sisin kobo matukar kana da Telegram account ka rike wa mining guda daya wuta ka dage sosai zaka samu jarin da zai taimakeka har karshen rayuwa Insha Allah Zaku ga mutanen da suke contact list dinku na kan waya suna ta bude Telegram account, sai dai ya kamata su san cewa Telegram suna da wasu sharuda wanda idan ka taka zasu iya rufe maka accoun, naga Muhammad King Cash ya bada shawara domin a kiyaye 👇 Sababbin masu bude Telegram wannan sakon gareku ne, ya kamata ku san tsauraran matakan da suke Telegram, ku sani Telegram ba wajan Chat bane kamar yadda akeyi a Whatsapp, Facebook da sauran Platforms, Telegram wajan Neman kudi ne na zamani wanda yake kan tsarin Web3  Domin gujewa asar...

ANƘARA ZUBAR DA KIMA DA MUTUNCIN NIGERIA A IDON DUNIYA

AN KARA ZUBAR DA KIMA DA MUTUNCIN NIGERIA A IDON DUNIYA Kowa dai yana sane da abinda ya faru kwanaki kadan da suka wuce tsakanin mahukuntan Nigeria da kamfanin Binance wanda ake hada-hadar kudin Crypto a cikinsa A wani yunkuri na borin kunya daga mahukuntan Nigeria sunce wai Binance ne ya haddasa hauhawar farashin Dala, don haka suka dauki mataki kan Binance, suka dakatar da P2P garemu 'yan Nigeria da muke mu'amala da Binance Exchanger Daga bisani Mahukuntan Nigeria sun kama ma'aikatan Binance guda biyu, amma ance wai daya daga cikinsu ya tsere ba tare da anyi bayanin hanyar da yabi yatsere ba Kwatsam yau kuma sai Shugaban gudanarwan kamfanin Binance ya saki labari cewa wasu daga cikin mukarraban Gwamnatin Nigeria sun bukaci kamfanin Binance ya basu cin hanci na kudi Dalar Amurka Miliyan 150, kusan Naira Biliyan 200 kenan a kudin Nigeria wai zasu gyara matsalar dake tsakanin Binance da Gwamnatin Nigeria  Amma Binance sunki yadda su bada cin hancin, sukace suna so a warware ...

BLOCKCHAIN TECHNOLOGY

        BLOCKCHAIN TECHNOLOGY  Writer:Abdul-Hadee Idan Ibraheem✍️ Da farko nayi niyyar in fito da wasu bayanai don in bayyana yadda masu Blockchain suke samun kuɗi masu yawan gaske, saboda 98 percent na wadanda suke Crypto basu yadda kudaden suke fitowa ba, hakan yasa naga wasu  wadanda basu san Blockchain ba suna cewa wai a ina ake samun irin wannan kudin da za'a yi ta rabawa mutane, har saboda rashin lissafi wasu suna kokarin Haramta abinda basu da sani akai.    ~ Daga jiya zuwa yau nayi ta ganin  posting din mutane da yawa, wasu ma abun dariya wai Malaman University, wasu da sunan Malaman addinin. Akwai abubuwan da suke gudana akan Blockchain behind the scenes wanda wallahi idan baka san Blockchain ba zaka yi ta hasashe ne kawai kana yin kuskure da nufin haramta abinda kai ka san baka sani ba.    ~ Ina jira ne kawai duk mai magana yayi magana, sai sun gama posting da rubutu da maganganu zamu zo mu fito da abun a fili, na rantse d...