Skip to main content

Posts

Showing posts from February, 2024

BABU HANNUN MU AKAN TASHIN FARASHIN KAYAN ABINCHI

Babu hannun mu a tashin farashin kayan abinci -- Dangote  Babbar Darakta a rukunin kamfanonin Dangote, Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta bayyana cewa rukunin kamfanonin Dangote ba su da hannu a tashin farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a kasar nan. A wata hira da Sashen Hausa na BBC, Hajiya Fatima ta ce kamfanin ya sayar da bangaren sarrafa abinci shekaru biyar da suka gabata ga Olam Group da ke sarrafa abinci da kasuwancin noma a Najeriya. Ta ce Olam a yanzu shi ne ke samar da fulawa, taliya, semolina, kuma duk wata fulawa da ake samu a kasuwanni ba kamfanin Dangote ne ke samar da ita ba. “A cikin yarjejeniyar cinikin, an amince da cewa za su ci gaba da yin amfani da sunanmu da tambarin muwajen yin kayayyakinsu, kuma nan da shekara mai zuwa za su daina. “Mu yanzu sukari, gishiri, da kayan yaji na Dangote kawai muke samarwa. Har ila yau, muna fatan za mu fara noman shinkafa nan gaba ko kuma badi,” in ji ta. Fatima ta kara da cewa ba su ji dadin yadda farashin kayayya

TYPES OF NETWORKS

Network category is determined by its size, the distance it cover and it's physical architecture. The types of networks are local area Network (LAN) and wide area Network (WAN).  A LAN normally covers an area less than 2 miles, a WAN can be worldwide.    LOCAL AREA NETWORK: A local area Network (LAN)  is Usually privately owned and links the devices in a single office, Building, or a Campus. Depending on the the of organization and the type of technology used, a LAN can be as simple as two PCs and a printer in someone's home office; or it can extend throughout a company and include audio and video peripherals.Currently, LAN size is limited to a few kilometers. WIDE AREA NETWORK : A wide area Network (WAN) Provides long-distance transmission of data, image, audio, and video information over large geographic areas that may comprise a country, a continent, or even the whole word. A WAN can be as complex as the backbones that connect the internet or as simple as a dial-

BABU INDA NACE NAFI ƳAN NIGERIA SHAN WAJALAR TSADAR RAYIWA

Shugaban rikunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya nisanta kansa da wani labari da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani cewa yafi yan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa. A jiya Laraba ne dai wani labari ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ake cewa wai Dangote ya ce ya fi yan Nijeriya jin raɗaɗin tsadar rayuwa. Sai dai a wata sanarwa da kamfanin sa ya fitar a jiyan, Dangote ya tabbatarwa da yan kasa cewa, wasu ne suka dauki nauyin yada labarin domin bata masa suna a daidai lokacin da Yan Najeriya ke cikin halin ‘kaka na kayi’ saboda wahalhalun da ake fama da su . Sanarwar ta nemi Yan kasar nan da suyi watsi da labarin, inda Dangote yayi fatan kawo karshen matsalar da ake ciki a Najeriya. “Duk abinda ya shafi yan Najeriya ya shafe mu”, inji Sanarwar. Dangote ya Kara dacewa, ”an kawo maganar faduwar darajar Naira da sayan kaya da Dala ne domin cimma wasu bukatu na kashin Kai bukatun da basu samu damar biya ba a baya.” Kamfanin na Dangote na sarrafa siminti da

RAGE KUƊIN AIKIN HAJJI 2024

Hukumar Alhazai ta Nigeria ta bada sanar War rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2024. Domin sauwaƙewa ƴan ƙasar. Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta samar wa maniyyatan Nijeriya ragin kudaden aikin hajjin 2024 daga gwamnatin Saudiyya. Rage kudaden, a cewar Fatima Sanda Usara, mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar, ya samu ne daga ɓangaren farashin kudin jirgi, da masauki da kuma zaman Masha’ir. Usara ta bayyana cewa an samu wannan nasara ne a lokacin da Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya jagoranci tawagarsa zuwa shirye-shiryen aikin Hajjin 2024 tare da mai da hankali kan rage farashin hidimomin da za a yi wa maniyyata daga Najeriya a ƙasar Saudiyya. Ta yi bayanin cewa shugaban ya gabatar da rokonsa na rage farashi kan yanayin tattalin arzikin duniya da ya shafi maniyyata, mahajjata daga Najeriya sakamakon kulle-kullen da ya faru lokacin COVID-19 da yakin da ake yi a Turai. Usara ta yi bayanin cewa farashin masauki a Madina ya ragu daga SR 2,080 (Ry