Skip to main content

SHAWARA MAI MUHIMMANCI GA WAƊANDA SUKE AIKI DA TELEGRAM


SHAWARA MAI MUHIMMANCI GA WADANDA SUKE AMFANI DA TELEGRAM ACCOUNT 
Datti Assalafiy ✍️

Yanzu dai a duniya shafin sada zumunta na Telegram shine yake tashe, sakamakon cewa yanzu babu wani shafin sada zumunta da ya bude hanyar da talaka fakiri zai samu alheri kamar Telegram

Ko baka da sisin kobo matukar kana da Telegram account ka rike wa mining guda daya wuta ka dage sosai zaka samu jarin da zai taimakeka har karshen rayuwa Insha Allah

Zaku ga mutanen da suke contact list dinku na kan waya suna ta bude Telegram account, sai dai ya kamata su san cewa Telegram suna da wasu sharuda wanda idan ka taka zasu iya rufe maka accoun, naga Muhammad King Cash ya bada shawara domin a kiyaye 👇

Sababbin masu bude Telegram wannan sakon gareku ne, ya kamata ku san tsauraran matakan da suke Telegram, ku sani Telegram ba wajan Chat bane kamar yadda akeyi a Whatsapp, Facebook da sauran Platforms, Telegram wajan Neman kudi ne na zamani wanda yake kan tsarin Web3 

Domin gujewa asara kar a kulle maka Telegram account, duk wanda kuka ga ya muku magana kuma baya cikin contacts list dinku to babu bukatar ku bashi amsa, domin hakan zai iya haifar maka shiga tarkon dokokin Telegram, sannan mafi girman matakin da zaka dauka shine kar ku kuskura ku dinga yiwa wadanda basa cikin contacts list dinku magana ta inbox a Telegram, imba haka ba robot na Telegram zai daukeka a matsayin dan damfara ya kulle maka account 

Ko Kuma kuga anyi adding dinku a wani group na Telegram ku dinga kokarin tura Link da sauransu, nan ma zaku iya samun matsala da Telegram account dinku

Nayi wannan rubutun ne saboda naga 'yan uwa da yawa sun bude Telegram, kuma dai nasan bai wuce kokarin fara neman alheri irin na Mining ba

Don Allah idan an ga wannan posting din, ayi kokarin isarwa zuwa ga 'yan uwa musamman wadanda basu san tsarin Telegram ba

Daga karshe ina kiranku zuwa cikin Telegram channel dina domin mu amfani juna da iznin Allah, ga link https://t.me/dattiassalafiyTech 

Allah Ya sa mu dace

Comments

Popular posts from this blog

ANƘARA ZUBAR DA KIMA DA MUTUNCIN NIGERIA A IDON DUNIYA

AN KARA ZUBAR DA KIMA DA MUTUNCIN NIGERIA A IDON DUNIYA Kowa dai yana sane da abinda ya faru kwanaki kadan da suka wuce tsakanin mahukuntan Nigeria da kamfanin Binance wanda ake hada-hadar kudin Crypto a cikinsa A wani yunkuri na borin kunya daga mahukuntan Nigeria sunce wai Binance ne ya haddasa hauhawar farashin Dala, don haka suka dauki mataki kan Binance, suka dakatar da P2P garemu 'yan Nigeria da muke mu'amala da Binance Exchanger Daga bisani Mahukuntan Nigeria sun kama ma'aikatan Binance guda biyu, amma ance wai daya daga cikinsu ya tsere ba tare da anyi bayanin hanyar da yabi yatsere ba Kwatsam yau kuma sai Shugaban gudanarwan kamfanin Binance ya saki labari cewa wasu daga cikin mukarraban Gwamnatin Nigeria sun bukaci kamfanin Binance ya basu cin hanci na kudi Dalar Amurka Miliyan 150, kusan Naira Biliyan 200 kenan a kudin Nigeria wai zasu gyara matsalar dake tsakanin Binance da Gwamnatin Nigeria  Amma Binance sunki yadda su bada cin hancin, sukace suna so a warware ...

BLOCKCHAIN TECHNOLOGY

        BLOCKCHAIN TECHNOLOGY  Writer:Abdul-Hadee Idan Ibraheem✍️ Da farko nayi niyyar in fito da wasu bayanai don in bayyana yadda masu Blockchain suke samun kuɗi masu yawan gaske, saboda 98 percent na wadanda suke Crypto basu yadda kudaden suke fitowa ba, hakan yasa naga wasu  wadanda basu san Blockchain ba suna cewa wai a ina ake samun irin wannan kudin da za'a yi ta rabawa mutane, har saboda rashin lissafi wasu suna kokarin Haramta abinda basu da sani akai.    ~ Daga jiya zuwa yau nayi ta ganin  posting din mutane da yawa, wasu ma abun dariya wai Malaman University, wasu da sunan Malaman addinin. Akwai abubuwan da suke gudana akan Blockchain behind the scenes wanda wallahi idan baka san Blockchain ba zaka yi ta hasashe ne kawai kana yin kuskure da nufin haramta abinda kai ka san baka sani ba.    ~ Ina jira ne kawai duk mai magana yayi magana, sai sun gama posting da rubutu da maganganu zamu zo mu fito da abun a fili, na rantse d...