BLOCKCHAIN TECHNOLOGY
Writer:Abdul-Hadee Idan Ibraheem✍️
Da farko nayi niyyar in fito da wasu bayanai don in bayyana yadda masu Blockchain suke samun kuɗi masu yawan gaske, saboda 98 percent na wadanda suke Crypto basu yadda kudaden suke fitowa ba, hakan yasa naga wasu wadanda basu san Blockchain ba suna cewa wai a ina ake samun irin wannan kudin da za'a yi ta rabawa mutane, har saboda rashin lissafi wasu suna kokarin Haramta abinda basu da sani akai.
~ Daga jiya zuwa yau nayi ta ganin posting din mutane da yawa, wasu ma abun dariya wai Malaman University, wasu da sunan Malaman addinin.
Akwai abubuwan da suke gudana akan Blockchain behind the scenes wanda wallahi idan baka san Blockchain ba zaka yi ta hasashe ne kawai kana yin kuskure da nufin haramta abinda kai ka san baka sani ba.
~ Ina jira ne kawai duk mai magana yayi magana, sai sun gama posting da rubutu da maganganu zamu zo mu fito da abun a fili, na rantse da Allah ba zasu iya kare abun ba, zamu fito da abun a ilimin Blockchain da ilimin Addinin Musulunci.
Duk ranar da nayi niyyar yin bayanin zan yi shi cikin misalan da zaka gane a fili a bayyane ko baka taba rike waya ba zaka gane.
Zango misali da abubuwan da kake gani a zahiri.
Sometimes nakan so mutanen mu suyi tambaya akan abu maimakon yanke hukunci, sai kaga mutum yazo yana cewa wai (idan kudin Halal ne toh a ina aka samu irin wannan kudi har ake rabawa mutane)...😅
~ Wallahi wanda yasan Blockchain dariya zai maka. Kudin da aka saka a cikin Notocin jiya Dala Biliyan Daya 1.1 ne, kasan nawa ne a Naira?
Naira Trillion dari 150 ne idan baka sani ba.
But duk ranar da nayi niyyar bayyana abubuwan a fili lokacin ne zaka gane a harkar Blockchain masu TON duk wata (monthly) sai sun samu fiye dashi, ba trading suke yi ba, ba saya ko siyarwa bane.
~ Amma a yanzu ba zamu ce komai akai ba, masu magana su gama maganar su tunda sun san komai akan harkar...😅
Ni kuma zanyi bayanin ne domin 'yan Crypto ba don masu sukan abun ba, domin in bayyana wa 'yan Crypto yadda abun yake dan kada wani ya jefa musu shubuha akan abinda shima bai san komai akai ba.
~ Anyway... Duk wanda yayi rubutu muna kallo, kuma muna jinjinawa kokarin sa...😅
Arewa kenan, mutanen...
Ni dai shawara ta itace a dan dinga neman ilimin abun sosai, yafi kazo Media kana rubutun da bayan shekaru 20 za'a iya gani a fahimci son zuciya ko jahilci ne yasa kayi magana akan abinda baka sani ba.
Allah yasa mu dace....
Comments
Post a Comment